User:Whitish Clouds LMS
©Whitish Clouds LMS Production
BAMBAMCIN RAYUWA DA KALUBALENTA GA MUTANEN DA DANA YANZU A AFRICA (YANKIN BAKAKEN FATA)
Daga: Kdjeart Ahsan, 2024.
TSOKACI
Yanayi ya kasance abu ne mai sauyawa daya danganci rayuwa, al'ada, addini da kuma zamantakewa. A bangaren rayuwa ana samun bambamce-bambamce wanda irin haka shike kawo sauyi da canji na rayuwar mutane. Irin wannan sauyin rayuwar yana afkuwa a wuraren duniya da dama, amma anfi fuskantar matsaloli da kalubale ga bangaren bakaken fata. Sauyin yanayi na duniya dana rayuwa abune da aka Saba dashi. Kuma ta hakane mutanen sauran kasashe in an debe wuraren bakaken fata ke bi don samar da cigaba a rayuwasu. Kasancewar ba'a ragemu ba ta bangaren arziki, amma didda haka rayuwar bakaken fata a koda yaushe tana zama ci baya ne. Hakan kan iya zama don yanayin halayyane ko kuma alhakin zaluncin da aka gudanar ga mutanen baya ya rinjayesu.
MAHIMMAN KALMOMI: Rayuwa, Kalubale, tsarkakakkiyar soyayya, Gaggawan nema, Yankin bakaken fata.
BAYYANA GODIYA
Ina mika godiya ga ubangiji daya tallafa man ya bani dama da albarka da basirar rubuta wannan sakon. Sana kuma ina mika godiya ga iyayena da membobi na shafin Wikipedia da suka bani kwarin gyuiwa kan cewar zan iya wannan rubutu a karona na farko na rubutu a harshen hausa. Ina ma kowo godiya, Allah ya albarkacemu da addininmu, iyayenmu da kasarmu baki daya.
1.0 GABATARWA
Rayuwar mutane a da sun kasance sunyita ne tare da gaskiya, tsarkakakkiyar soyayya, adalci, rikon Amana da takatsantsan wanda tabbas an rasashi ga mutane masu tasowa. Ga mutanen yanzu, tsallake hanya da wayon da yafi misali ya gurbata tunaninsu. Sun kasance basu iya kiyaye iyakokin kansu bama balle na ubangiji wanda hakan yasa aka sallada masu tsoro da firgici da rashin natsuwa a rayuwarsu. Kamar yadda aka fada a Al-qur'ani,
'Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsawa da walkiya: suna sanyawar yatsunsu a cikin kunnuwansu daga tsawarwakin, domin tsoron mutuwa. Kuma Allah Mai khwayewa ne ga kafirai!' (Suratul Baqara; Aya ta tara).
Rayuwa ta kasance aba ce ta Samar da darussa, kalubale, da ilimi a cikinta. Duk wanda ya kasance a cikin rayuwa musamman ta duniya to tabbas zai koyi sababbin abubuwan da a da bai sansu ba. Duniya an halicceta ne da bangarori da dama kasancewar ba ta mutane kadai bace. Akwai halittu da dama a cikinta wanda har yanzu ba'a kai ga saninsu ba duka. Ga tsarin rayuwa ta mutane sun kasance masu aiwatar da abubuwa iri guda in an fidda bangaren bakaken fata. A dalilin bambamci na rayuwarsu sun kasance daban daga sauran kalolin mutane da suka hada da farare wato larabawa da kuma jajaye wato turawa. Akwai tambayoyi da dama da suka tsayawa sauran mutane dasu kansu bakaken fatar, ko meyasa suka bambamta ta bangaren rayuwarsu da dabi'arsu?
Sanin kowane dabi'u da halaye abu ne daya kasance Kamar kaddara ga kowace halitta, ga mutane, dabbobi, tsuntsaye da sauran halittun boye. Akwai wa'enda suke son kansu don halayensu, akwai kuma masu kin kansu don halayensu. Don haka bai kamata a ta'allaka munanen halaye ga kowane bakar fata ba. Ta iya yiyuwa a samu mutanen farar fata ko jajjayar fata da munanen hali, kuma za'a iya samun bakaken mutane da halaye masu kyau. Wannan halittarmu ce kuma kaddararmu, shiyasa aka fada cewa an halicci mutum mai aikata kuskurene. Kuma da albarkar ubangiji ya sanya yafiya ga duk bayin da suka nemi gafararsa game da kuskuransu. Don zuciya aba ce wacce take tamkar katanga ga gida. Jiki shi ya lullubetane amma zuciya tabbas itace mutum baki dayanshi. Tare da ita aka haliccemu kuma a kanta zamu cigaba da tafiya. Wannan ne yasa akafi rinjayar bincike na halaye da dabi'a a kan kyau ko matsayi. Sau da yawa ana samun halitta mai kyau ta lullube bakar zuciya, kuma ana samun halitta sabanin hakan ta lullube farar zuciya. Kuma ga sa'a ana samun halitta kyakkyawa ta rufe farar zuciya. Ga zukatan mutane bakar fata sun zama masu rike abu guda mafi mahimmancin da yafi rayuwarsu da imaninsu, wato 'KUDI'. Kudi dole ana bukatarshi don inganta rayuwa amma ba lalle ya samar da komai ba. Mafi munin abinda bakaken fata a zamanin yanzu suka saka a zukatansu shine, 'GAGGAWA DA YAWAN GURI'. A zamanin da, mutane suna jajircewa haikan ga abinda suke da guri kansa. Guri ba zai zama muni ba a rayuwa don dukkan rayuwa da zamani na tafiyane da guri. Amma sabanin mutanen yanzu masu tasowa, sun kasance masu bukatar cika guri da gaggawa kuma ba tare da sun wahala ba. Wannan shine daya daga cikin kalubalen da bakaken fata ke fuskanta a rayuwa kuma ya zama abinda ya tauye ma jikunnansu hakki wurin cigaban rayuwarsu.
1.1 MANUFOFI
A karshen wannan adabi, mutane zasu fahimta kuma su iya;
1. Sanin dalilin da ya kawo sauyi da bambamci ga rayuwar mutanen bakaken fata da sauran jinsin mutane.
2. Fahimtar rayuwa da abinda ke cikinta dake kawo natsuwa da akasinta.
3. Bangaren zamantakewar mutanen Africa musamman ga bakaken fata.
4. Hanyoyin da zasu gyara dabi'un mutanen bakaken fata.
5. Abinda zai kawo sauyi ga duniya dangane dasu.
1.2 NAZARIN TAMBAYOYI
1. Meya kawo bambamci game da dabi'u da rayuwar mutanen bakaken fata?
2. Kasancewar ba'a ragi mutanen bakaken fata da komai ba ta bangaren arziki, halitta da nagarta meyasa suka samu nakaso ta bangaren kima da kishi?
3. Meyasa mutanen bakaken fata suka zama bare, ababen kyama a duniya daga kowacce halittar bil Adam?
4. Kalubalen rayuwar mutanen bakaken fata kan iya zama don yanayin halayyarsune ko kuwa kishin dake garesu suka bari ya gushe?
5. Zai iya yiyuwa alhakin mutanen da aka zalunta ne ya saka mutanen bakaken fata cikin wakala da rashin aminci dangane da cewar ba haka mutanen bakaken fata da suka gabata sukayi rayuwarsu ba?
6. Menene takamaiman bambamcin rayuwa na mutanen bakaken fata a zamanin da dana yanzu?
2.0 BITA A KAN ADABI
2.1 BAMBAMCIN RAYUWA DA KALUBALENTA GA MUTANEN DA DANA YANZU A AFRICA (YANKIN BAKAKEN FATA).
Mutanen bakaken fata yanzu sun kidime kan son dukiya da duniya ba tare da damuwa mutunci ko kima ba, sabanin mutanen da. Hakan ya kasance baga ma'aurata ba, ba ga iyalai ba, ba ga makwabta ba, kuma ba ga yan kasuwa ba da sauran mutane. Irin wannan yanayi babbar matsala ce dake janyo debewar albarka da tausayin ubangiji ga mutane da kasa baki daya. Sakamakon haka yasa aka debe kwarjini, Amana da kwanciyar hankali garesu.
'Akwai wani salihin mutum mai arziki. Ya kasance bai damu da abinda wasu ke ciki ba. Kuma ya zama mai bada kyauta ga mutane ba adadi. Ana cikin wannan yanayi sai wata rana wuta ta kama gidansa da iyalensa a ciki. A wannan lokacin Kuma mutumin baya gida, yana wurin aikinsa. Cikin sa'a iyalenshi suka tsira ba'a rasa rai ba, amma sai ya zama duk kayen gidan makwabtansu sun sace wurin kawo dauki. Bayan hakan, sai ya zama ga wannan salihi arzikinsu ya ragu ta yadda basu iya bayar da abinci ga mutanen waje. To hakan yasa makwabtan suka dinga jifarsu da maganganu mararsa dadi saboda rashin abinda suka saba basu'. Yanzun duba da cewar ya kasance mai taimaka masu, meya dace su saka masu dashi? Saka alkairi ga kyautatawa ibada ne. Amma Sam wasu mutanen basu san da haka ba. Idan muka koma bangaren ma'aurata da samari, aure ga mutanen bakaken fata tamkar tsinko baure ne daga icce. Da zarar sum gama amfana da abu, basu duba tare. Wannan halayyar ko a dabbobi ba'a cika samunta ba. Haduwar soyayya ta gaskiya da amana abune wanda ba zai taba gushewa ba indai da sanin karamci da daraja. Amma abun mamaki, aure ya zama ba amana ko yarda a cikinsa, a sadda kowa ke neman sa'ar kowa, bi lungu da sako kan yin asirce-asirce, binne-binne, tsallake iyakoki kawai kuma a kan samun iko da mulkin gida. Idan ga masu mulki ne suma kowa na nashi, haka ga ma'aikata da dalibai. Ko meyasa hakan?
Mafiya yawan mutane sun zama tare da yan'uwansu tamkar anci moriyar ganga. San zuciya ya mamaye kowa, baga samarin ba ko yan matan kuma ba ga mazan ba ko mata. Wannan ne daya daga cikin kalubalen rayuwar mutanen bakaken fata. Al'adar da suka watsar shine wanda sauran wasu mutane na wasu jinsin basu barsu ba kuma har yanzu yasa suka zama cikin zaman lafiya. Amma ko ga wuraren da ba wurin bakaken fata ba, daukar wannan dabi'a kan afkar da matsaloli da masifu ga jama'a da duniya baki daya.
'Akwai wasu gurbatattun mutane da suke samar da matsaloli a wurin aikinsu, daya daga cikinsu anace dashi Baure, guda kuma ana kiransa da Dosa. Baure da Dosa dukkansu suna aikin kamfani ne, amma kokarinsu suga sun saka kamfani matsala ba tare da tunanin kansu ba didda a cikin suke samun rayuwa, sutura da kula da iyalensu. Su kawai bakin cikinsu kar mai kamfanin, Mr. Paul Senis ya daukaka. Wannan wane irin kungurmin jahilci ne! Ana cikin haka sai akayi sa'a Mr. Paul ya san ta kan sharri. Sai ya hada kai da wanda yafi iya yin sharri wato Dosa, ya kara mashi matsayi na zama mai kula da harkokin shige da fice na kamfanin ba tare da ya hanninta mashi lasisi ba. Dosa yayi farin ciki sosai a inda kuma ya dinga yin nesa tare da kula da abokinsa. Yana tsoron kar Baure ya ha'inceshi kamar yadda suka dinga yiwa Mr. Paul a baya. A haka ya kulle duk wasu kafofin samayya da ada suke cuta wurin samunshi tare. Baure abu yayi mashi yawa, gashi haramun taki samuwa bayan baya wadatuwa da halalinsa. To sai ya fara yima Dosa zagon kasa tare da kokarin tona mashi asiri. Dama Mr. Paul ankare yake dasi dayake dan Asian ne. Jayayya ta cigaba da afkuwa a tsakaninsu har ta kai Baure ya tona asirin duk abinda sukayi har abinda suka shirya yi nan gaba. Hakan tasa aka kori Baure ba tare da an kori Dosa ba. Mutane zasuyi ta mamaki ya za'ayi hakan? Didda sun kasance masu aikata kuskure, amma akwai hanyar da za'a iya tsaida iyakokinsu da niyyarsu. Samun Dosa cikin kamfanin babban mataki ne da zasu iya yaki da makirai irinsa saboda mai neman kaya a kifi sai ya fasashi kana zai ganta. Huddar Dosa tare da mutanen kirki zai iya sauyashi ya dawo mutumin kirki. Amma barinshi tare da Baure, to ko dai abu mafi muni ya faru (a aikata kisa wurin gurin mallakar wani abu) ko su karya kamfanin da manajan baki daya'.
Tabbas rayuwar mutanen bakaken fata abune mayuwaci. Sune suke;
– Bada rayuwarsu da ta iyalensu ga makiyansu cikin sauki da farin ciki.
– Iya juya baya ga masoyansu ba tare da yin tunani ba.
– Iya bada abun hannunsu ko su lalata abu koda suna amfana dashi.
– Bada gamsashiyar yadda ga bare a kan na gida.
– Rashin sanin kima da darajar halitta, lokaci da sirri.
– Ganin manyansu da kansu kai daya (wato rashin mutunta jama'a har da iyaye).
– Rashin son cigaba ga wasu inba kansu ba ko da abinda za'a samu zai amfanesu. Kamar a kasa, zasu iya gina wasu kasashen da amfanin kasarsu ba tare da sun damu su kyautata nasu muhallin ba, wato burga damo kenan.
– Iya tunkuda yaransu a rijiya su rufeta. Da dai sauransu.
Ba duka aka taru aka zama daya ba. Sai dai anfi yawan samun irin wa'ennan halayen a cikinsu.
3.0 HANYA (METHODOLOGY)
A tushen akan takamaiman fassarar wannan adabi, an samu nasara game da wannan bayanai;
1. Samun hanyoyin gyaruwar rayuwa ga mutanen bakaken fata.
2. Sanin dalilin da yasa mutanen bakaken fata suka zama kamar mujiya cikin yan'uwansu.
3. Sanin ko su wanene kabilar bakaken fata daya zama a da daga garesu ake samun masu fasaha da basira da alkairai na rayuwa.
4. Kalubale a kan canjin rayuwar mutanen bakaken fata inda a da sun kasance mafi yawancinsu mutanen kirkine masu gaskiya da rikon amana da jajircewa, amma a yanzu anfi samun gurbatattu a cikinsu. Wanda hakan ya jawo tabo garesu a rayuwa.
5. An samu sanayya kan cewar a kowane jinshin halitta ana samunsu da dabi'u da halaye daban-daban, mai kyau da marar kyau.
4.0 SAKAMAKO
4.1 BAMBAMCIN RAYUWA DA KALUBALENTA GA MUTANEN DA DANA YANZU A AFRICA (YANKIN BAKAKEN FATA).
Son zuciya da neman kudi ido rufe masifa ne. Ya kasance a silar hakan mutane da dama sun halaka, wasu a duniya wasu kuma a lahira tun daga wa'enda ke cutarwar da wa'enda ake cutarwa baki daya. Mafi yawanci dan-Adam kan iya kauce hanya don samun duniya da kudi. Kuma mafi yawanci anfi samun mutanen bakaken fata da wannan halim bayan sun manta da cewar dukiya abune wanda yake tamkar gawayi. Kamar misali, ka sami gawayi wanda zakayi amfani dashi shine dacen. To amma da zarar ya gama amfaninshi, zai zama toka ne ya hure. Har zakayi mamakin cewar rayuwar dan-Adam kamar haka take. Abinda zaiyi saura daga gareshi bayan mutuwarsa shine wani karamin kashi na tsakkiyar baya, sai dabi'unsa da ayyukansa. Ba'a taba lissafo dukiya cikin nasarar rayuwa ba, face samun dace da jajircewa. A duniyarmu dole sai da kudi kuma akwai hanyoyin samunsu cikin sauki ga wa'enda Allah ya sawwakawa rayuwa. Yin imani shi yafi ga komai. Saboda zakuga idan Allah yayi a cikin sauki zaka rayu ka mutu, to har abada haka zai kasance gareka. Kuma idan Allah yayi cikin wahala zaka rayu ka mutu, to komin dukiya da mulkin daka nacewa nema sai dai ka tarawa wasu wa'enda ko a lahira ba zasu amfaneka da komai ba. Koda zakaji dadin dukiyar, to kalilan ne kuma a duniya kadai, radadin abinda zaka tadda a dalilin hakan ba mai yankewa bane. Allah ya kiyashemu.
5.0 TATTAUNAWA
Bambamcin rayuwa da kalubalenta ga mutanen da dana yanzu a Africa abune mai tazarar gaske. Bada tabbaci a kan gyaruwar gurbacewarta sai Allah, da kuma bangaren sauyi daga mutanen da sukayi niyyar canzawa zuwa halaye masu kyau. Kowace halitta a sanin kowa nada nata rabon da Allah ya tsaga mata. Rai da ruhi ba zasu taba barin gangar jiki ba har sai an gama mallaka mata rabonta na duniya da kuma bata ikon tanadin lahira. Mutane musamman na Africa sun kasance a da mutanene da ake bawa girma da mutunci saboda sune suka taso suna nema, sai ubangiji ya taimaka masu wurin cika masu shi. A kan yanayin da mutanen yanzu suka dauki rayuwarsu daya bambamta dana da. Sun zabi dukiya a kan komai sai ubangiji ya barsu da ita, basu ga kwanciyar hankalin kuma basu ga farin ciki. Ko kun San cewa ka zauna a karamin gida cikin kwanciyar hankali, farin ciki da wadatar zucci ga duk abinda ka samu komin kankantarshi yafi gareka daka kasance a babban gida cikin hankali da damuwa da kunci.
Akwai sirrika da dama da ubangiji ya lullube a garemu. Didda an halittaka da bakar fata, sai aka hore maka basira da hazaka da tafi ta kowanne jinsi don ka inganta rayuwarka tafi ta kowa. Amma sai dai ...